//
Thursday, April 2

Iyalan Buhari na da damar daukar jirgin shugaban kasa suyi harkokin gaban su -Garba Shehu

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammad Buhari, Malam Garba Shehu ya bayya cewa iyalan shugaban kasa n lasisin hawa jirgin fadar gwamnati domin halartar kowane taro.

Garba Shehu yayi martani ne game da masu kace nace a kan amsa gayyata da diyar shugaban kasa, Hanan Buhari tayi na halartar bukukuwa a jihar Bauchi da sarkin garin, Lirwanu Adamu yayi a ranar Alhamis.

Rahoton Dabo FM ya jiyo Garba yana fadin kwarai diyar shugaban kasa ta bukaci jirgin, wanda aka sanarwa da ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan fannin tsaro, inda daga nan aka sahale mata yin amfani da jirgin.

Ya kuma kara da cewa “A doka shugaban kasa, mataimakin sa, shugaban majalisar dattijai da na wakilai duk doka ta bawa iyalan su dama na yin amfani da jiragen fadar gwamnati.” Kamar yadda TheCable ta fitar.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020