Jami’iyyar APC a matakin jiha ta jihar Kano, ta jaddada hukuncin dakatar da dan Majalissar Tarayya mai wakiltar Bebeji/Kiru daga jami’iyyar na tsawon watanni 12.
Hakan na zuwa ne bayan kwamitin bincike da uwar jami’iyyar a jihar ta kafa domin yin duba game da zargin Hon Abdulmumin Jibrin na yiwa jami’iyyar zangon kasa a zaben da ya gabata.
Sanarwar da sakataren jami’iyyar, Ibrahim Zakari Sarina ya sanyawa hannu tace jami’iyyar ta fitar da hukuncin ne bayan zaman tattaunawa da binciken data gudanar.
“Kwamitin bincike n jami’iyyar ta goyi da bayan dakatar da Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa, dan Majalissar Tarayya mai wakiltar Bebeji Kiru na tsawon watanni 12.”
“Hukuncin dakatarwar ya fara daga ranar 12 ga watan Agustar 2019.”
