Kada Atiku ya yarda da sakamakon zabe, domin magudi akayi – Dr Ahmad Gumi

Karatun minti 1

A wani sako da Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya wallafa a shafinshi na facebook, yayi kira ga Alhaji Atiku Abubakar da yakai kara kotu akan rashin yadda da sakamakon zabe.

Malamin da a kwana kwanannan aka jiyo da kausasan kalamai na sukar shugaba Buhari tare da magoya bayanshi.

Shiekh yace dolene a yabawa Alhaji Atiku Abubakar bisa yadda ya kasance mai bin dukan dokakin da gwamnati ta gindaya na zabe.

“Ina kira ga Atiku, da karya yadda da sakamakon zaben da aka fitar, domin karya goyi bayan karya, yakamata ya shiga kotu domin neman adalci kamar yadda Buhari yayi a lokutan da yayi yana neman zabe.”

Sheikh ya kara da cewa dolene ayi gyare-gyare a hukumar INEC domin kaucewa faruwar goyuwa da rashin adalci a kowanne mataki.

Ya nuna rashin jin dadinshi bisa yadda aka rika siyan kuri’ar mutane musamman na arewacin Najeriya, inda yace ana siyan kuri’un akan Naira 500.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog