Siyasa

‘Yan Najeriya sun yanke hukunci, NNPC ta huta?, Buhari yaci zabe.

Anan za’a iya cewa karshen tuka-tikin kik, wai kurunkus dan kan bera, bayan gabatar da zaben shugaban kasar Najeriya a 23 ga watan Fabarairun 2019, ta faru ta kare shugaba Muhammadu Buhari ya kara dafewa kan karagar mulki.

Zaben daya gabata, zabe ne mai matukar jin dadi da farinciki, yacce al’umma suka fito akayi zabe lafiya aka gama lafiya, musamman a arewacin Najeriya, inda ba’a samu koda wata hayaniya mai karfi ba balle a aje maganar rasa rai ko dukiya.

Kamar yadda aka saba, shugaba Buhari yasha ruwan kuri’u daga yankunan arewa baki daya tare da wasu yankunan na yarabawa.

Masu sa’ido akan ganin sahihancin zaben sun bada tabbacin sahihancin zaben, bayan da sukace zabe ne a gaskiya.

Sai dai wannan karon ma iya cewa jihar Rivers bataji dadin tsauraron tsaron da aka saka wajen ganin anyi zaben gaskiya ba, inda jihar ta gaza baiwa jami’iyyar PDP kuri’un da suka bata a waccen kakar data wuce, sun sha ta arangama da sojoji akan korarinsu na chanza zaben zuwa karin kuri’un wanda gwamnatin jihar ke marawa baya.

Batun siyarda kamfanin NNPC, yanzu ka iya cewa ruwa ta sha.

Sai dai jami’iyyar PDP tace bata yadda da wannan zaben da aka gudanar ba, kuma tana shirin shiga kotu domin kai karar hukumar zabe ta INEC.

Karin Labarai

Masu Alaka

Dole ‘yan Najeriya su dena fita kasashen waje don neman magani -Buhari

Dabo Online

Tirkashi!: Wani Bakatsine ya canza sunan sa daga Buhari zuwa Sulaiman

Muhammad Isma’il Makama

Ƙurunƙus: Buhari ya hana ministoci zuwa yawon gantali ƙasashen waje

Muhammad Isma’il Makama

Kano: Dole a fadi sakamakon zabe kafin sallar Isha – Kwamishina Wakili

Wacce Kabila ce bata morar gwamnatin Shugaba Buhari?

Dabo Online

APC ce ta lashe zaben Kano kuma ta tabbatarwa Kotu – Buhari

Dabo Online
UA-131299779-2