Ban amince da zaben 2019 ba, kuma sai na kai kotu

Karatun minti 1

Tsohon dan takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jami’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yace bai yadda da sakamakon zaben 2019 ba.

Alhaji Atiku Abubakar ya wallafa bayanan kin amincewa da sakamakon zaben a shafinshi na facebook da safiyar yau Laraba.

Yace tinda aka fara mulkin dimokradiyya a Najeriya, 2019 ce shekarar da aka ci mutunci dimokradiyya ta hanyar hanata aiki.

Daga cikin abinda yace suka sakashi kin amincewa da sakamakon shine, dirke sojoji da akayi masu yawan gaske a garin Rivers, Akwa Ibom da  Lagos.

Ya kara da cewa anyi amfani da sojojin ne wajen yin barazana ga al’ummar yankunan domin kauracewa guraren zabe.

“Idan da ace anyi sahihin zabe, to tabbas a matsayi na dan dimokradiyya, dole zan mika wuya tareda taya wanda ya samu nasara murna.”

“Ban yadda da zaben 2019 ba, kuma zan kalubalanci zaben a kotu.”

Ina tabbatar da al’umma baza mu taba bari a ki baiwa dimokradiyya hakkinta ba.

 

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog