Kamar kullum, Buhari ya yi Allah-wadai da kisan manoma 43 a Borno

Karatun minti 1

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da yankan ragon da wasu ‘yan binduga da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka yi wa manoma a jihar Borno.

DABO FM ta tattara cewa mayakan kungiyar sun yanka manoman ne a safiyar Asabar ya yin da suke girbin shinkafa a kauyen Kwashebe da ke karamar hukumar Jere a jihar.

Da yake bayyana rashin jin dadinsa kan kisan kamar yadda ya saba, shugaba Buhari ya ce kisan da mayakan suka yi wa manoman abin Allah-wadai ne, ya kuma bayyana kisan a matsayin aikin hauka da tumasanci.

“Ina Allah-wadai da kisan da ‘yan ta’adda suka yi wa manomanmu masu kwazo a jihar Borno. Wannan kisan na rashin hankali ya kuntata wa Najeriya baki daya.”

“Ina taya alhini da addu’a ga iyalansu a wannan lokaci na bakin ciki. Allah sa sun huta.”

Shugaban ya bayyana hakan ne ta hannun babban mataimakinsa a harkokin yada labarai, Mallan Garba Shehu.

DABO FM ta tattara cewa bayanan shugaba Buhari suna zama kamar maimaici a duk lokacin da aka yi sa a ya yi jaje ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a arewacin Najeriya.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog