Kannywood: Mawakan APC sun zargi Rarara da handame kudaden kungiyar da aka tara

Hatsaniya ta barke a masana’antar Kannywood daga ‘yayan kungiyar Mawakan Arewa na jami’iyyar APC biyo bayan zargin da ake yiwa daraktan waken yakin neman zaben shugaba Buhari, Dauda Kahutu Rarara tare da wadansu mutane 7 da cinye kudin kungiyar.

Fusatattun ‘ya ‘yan kungiyar da suka kafa kwamitin mutane 11 wanda mataimakin shugaban kungiyar ke shugabanta, Murtala Mamsa, Ahmad Turaki Kaka a matsayin sakatare sun gayyaci Rarara tare da mutane 7 da ake zargi domin wanke kansu tare da hujjojin barranta daga zargin da akeyi musu.

DABO FM ta rawaito daga DAILY TRUST cewa kungiyar ta kaddamar da kwamitin ne a satin daya gabata biyo bayan wata ganawar gaggawa da shugabanninta na jihohi 19 suka aiwatar.

Sakataren kwamitin, Ahmad Turaki Kaka, yace dole ne ayi bincike saboda yawan korafe-korafe da ‘ya yan kungiyar suka kai gaban kungiyar da sama da fadi da kudaden da aka hada daga gudunmawar wasu mutane, masu taimako tare da wadansu hukumomi.

Kwamitin ya gayyaci; Haruna ABdullahi Ningi, Haruna Baban CHinedu, Ibrahim Yala, Isiyaku FOrest, Alfazazee, Kamilu Koko da Baba Yanmedi.

Rarara yaki amsa kira da sakon karta kwana da wakilin DAILY TRUST yayi masa, sai dai mai magana da yawunshi, Aminu Afandaj yace basu da masaniya akan gayyatar da kwamitin yake yiwa Rarara.

“Bamu da masaniya akan gayyatar, amma zamu amsa a duk lokacin da takatardar ta iske mu.

DABO FM ta binciko cewa tini dai Haruna Baban Chinedu ya amsa karbar takardar gayyata daga kwamitin da kungiyar ta kafa, kuma ya bayyana cewa zai hallara a gaban kwamitin.

Wannan ne karo na 2 da ake zargin Rarara da mutanenshi da hamdame kudaden kungiyar.

Idan ba’a mantaba, a watan Yulin 2018, wasu daga cikin ‘ya ‘yan kungiyar da sun Zargi Rarara da mukarrabanshi da yin sama da fadi da Naira miliyan 100 da kungiyar gwamnonin Arewa ta bawa kungiyar mawakan.

%d bloggers like this: