Kano: Ganduje ya tsige Sheikh Daurawa daga mukamin kwamandan Hisbah

dakikun karantawa

A jiya Talata, 19/02/2019, wasu majiyoyi daga jihar Kano suka rawaito matakin da gwamnatin jihar Kano karkashin Dr Abdullahi Umar Ganduje, khadimul Islam ta dauka na korar babban sakataren Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa daga ofishin Hisbah dake birnin Kano.

Majiyoyin gani da ido sun tabbatar da wasu jami’an gwamnati da ba’a bayyana ko suwaye ba sunyi dirar mikiya a ofishin na Hisbah dake unguwar Sharada.

Sunyi fatali da kayan sakataren kwamanda, tare da umarnin ficewa daga ofishin bisa umarnin gwamna.

Jami’an basu tsaya daga nan ba, suka nufi ofishin na kwamanda, suka fito masa da wadansu litattafai tare da zarkamawa ofishin wani zabgegen kwado.

Ko menene dalilan  daya sa gwamnatin ta dauki wannan matakin na yiwa Sheik kora da hali?

Al’umma da dama sun dade suna shakkun dangantakar da take tsakanin tsagin gwamnatin da kuma Sheikh, domin Sheikh yakan fito ya soki gwamnatin a duk sanda ta kauce.

Sheikh yayi magana akan rashin zuwan hukumar Hisbah lokacin da ake shagul-gulan bikin Fatima Ganduje, bikin daya zanyo hankalin al’ummar Kano baki daya, akan yadda aka tafka badala a wannan bikin.

Inda yace hukumar Hisbah, hukuma ce da gwamnati ta kafa, kuma idan suka shiga domin hana wannan shagalin bikin, gwamnatinka iya rushe ita wannan hukuma ta Hisbah.

Lokacin da Sheikh yayi magana akan faifayen bidiyo da aka ga gwamna yanata sinkime daloli a aljihun babbar riga, Sheikh yace yakamata mahukunta suyiwa faifan duba na tsanaki.

“Idan an kama gwamna da laifi yakamata a hukunta shi, idan bashida laifi, a jawa dan jarida kunne saboda gaba.”

A makon daya gabata, Sheikh ya jaddada goyon bayanshi ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, shine babban dan hamayyar gwamnatin Ganduje, lamarin da yayi tsamari a tsakanin tsohon gwamnan da gwamna Ganduje.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog