Zaben2019: Ina kiran magoya bayana da su zabi shugaba Buhari – Salihu Takai

Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin inuwar jami’iyyar PRP, Mal Salihu Sagir Takai yayi kira ga magoya bayanshi da su zabi shugaba Muhammadu Buhari a matakin shugaban kasa.

Mal Salihu yayi wannan kirane ta hannun mai magana da yawunshi, Auwalu Mu’azu, yace sunyi wannan kira ne biyo bayan rashin jin dadinsu na dage babban zabe da hukumar INEC tayi.

“Duk da dage zabe da akayi, ya zama wajibi ayi kira ga al’ummar kasa da kada suyi kasa a gwiwa wajen kara fitowa dangwala kuri’asu.”

Daga karshe yayi kira ga dukkanin magoya bayanshi dasu zabi shugaba Muhammadu Buhari domin cigaban aiyukan alheri da shugaban ya fara, inji Mal Salihu Sagir Takai.

Masu Alaƙa  Zaben2019: Duk bakin cikin su sai na siyar da NNPC - Atiku Abubakar

 

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.