Mon. Nov 18th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Kashi 6 cikin 10 na matan Najeriya, sunada tabin hankali -Masana Kwakwalwa

1 min read

Wani malamin jami’a, Dr Auwal Sani Salihu, yace kashi 6 cikin 10 na mata, da kuma kaso 4 cikin goma na maza a  Najeriya sunada tabin hankali.

Dr Auwal ya bayyana hakan ne a wani taron bita da asibitin kula da kwakwalwa na gwamnatin tarayya dake jihar Sokoto ya shirya.

Ya kara da cewa babban abinda yake kawo tabin hankali shine mu’amala da miyagun kwayoyi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Dr Auwal Sani, malamine a jami’ar Bayero dake Kano.

Dr, ya kara da cewa, akwai cututtuka sama da 300 masu alaka da ciwon hauka, wadanda ka iya kasancewa sunzo da sauki, tsaka-tsaki ko ma suzo da karfin gaske.

“Kaso 80 sune ke zuwa da sauki, 20 masu tsananin gaske.”

Dr Auwal, ya kara da cewa, ciwon hauka ba ciwo bane dauwamamme, akan magance shi an samu kulawa mai kyau.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.