(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Kwankwaso zai iya biyan kudin makarantar dalibai 370 daga cikin kudaden daya karba a majalissar dattijai – Bincike

dakikun karantawa
Rabiu Musa Kwankwaso

Tsohon Sanatan Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Engr. Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya bude gidauniyar da take da kudirin fitar da dalibai ‘yan jihar Kano kasashen waje domin karo karatun digiri na 2.

Sai dai DABO FM binciko cewa gidauniyar ta shigo da sabon salo, inda Kwankwaso ya bayyana a wata hira da yayi da gidajen rediyon jihar Kano cewa za’a nemawa gidauniyar kudi tare da kira ga duk ‘yan kishin kasa su kawo gudun mawa.

A Ranar Asabar, gidauniyar ta kaddamar da shirin fara tara kudin wanda alkaluma suka nuna cewa gidauniyar ta hada daruruwan miliyoyin kudade da manyan jihar Kano dama wasu na waje suka bayar.

Sai dai ayar tambayar anan shine, daga cikin kasashen da Kwankwaso ya ayyana gidauniyar zata tura dalibai akwai kasar Indiya, kuma binciken DABO FM ya binciko wata makaranta da Kwankwaso zai kai daliban mai suna Mewar University da ke da zama a jihar Rajasthan na arewacin Indiya.

Mun binciko kudin makarantar da kudaden dakunan kwana wadanda daliban zasu zauna a cikin makarantar, wanda idan aka lissafa kudin, Kwankwaso zai iya biyansu shi kadai daga cikin kudaden da majalissar dattijai ta bashi wanda hakkin al’ummar Kano ta tsakiya ne.

Jaridun kasa Najeriya dama wasu na duniya, sun rawaito tsohon Sanata Shehu Sani ya bayyana kudaden da kowanne Sanata yake karba.

Kowanne Sanata yana karbar zunzurutun albashi da alawus da kimanin Naira Miliyan 14.25.

Kowacce shekara Kwakwaso yana karbar:

Albashi: N9,000,000 (Miliyan 9)

Alawus: N163,000,000 (Miliyan dari da sittin da uku)

Kudaden aiki a yankin Kano ta tsakiya: N200,000,000 (Miliyan dari biyu)

Idan ka lissafa, jimillar abinda yake karba a shekara ya kama N372,000,000.00 (Miliyan dari uku da saba’in).

 

Wa’adin kowanne Sanata a Najeriya, shekara 4 ne, sai a lissafa kudaden har na tsawon shekaru 4. 

Zai kama N1,488,000,000 a tsawon shekaru 4.

 

Ga jerin kudin jami’ar Mewar University Chittogarh

Kudin Karatu ; $530-600 (N165,000-N187,200)

Kudin dakunan kwanan dalibai ; $1000-1500 (N312,000 – N468,000) + Abincin safe, rana da dare.

NB: Jami’ar tana bada $500 (N156,000) ga  duk wanda ya samawa sabon dalibi gurbin karatu.

NB 2: Dalibi yana da damar fita don zama a dukunan makaranta bayan wata 6, ana biyan N237,600

DABO FM ta hada cewa Kudin dalibai 370 a jami’ar Mewar zai kama N‭69,264,000‬ (Dala 600 kowanne dalibi) a kowacce shekara na tsawon shekara 2 da akeyi a yin digiri na 2. Jimillar kudin zai bada N138,528,000‬.

Kudin dakunan kwanan dalibai 370 zai kama N‭115,440,000‬ (dala dubu 1 kowanne dalibi) ko N173,160,000 (dala dubu 1500 kowanne dalibi). Jimillar kudi a shekara 2 zai bada N230,880,000‬ – N346,320,000‬.

Akwai alawus da ake bawa dalibai saboda bukatu duk wata, duk dalibin da yake zama a dakin kwanan dalibai ana bashi abincin safe, rana har dare.

N50,000 zata ishi dalibi har ya mike kafa a kowanne watan duniya indai a kasar Indiya duba da cewa dalibin bashi da matsalar biyan kudin dakin kwananshi a cikin 50,000 din.

Kowanne wata in za’a basu N50,000, kudin zai kama N‭18,500,000‬ ga dalibai 370. Wanda jimillar kudin zai zama miliyan ‭N444,000,000 a watanni 24.

Zaka fiskanci cewa gaba daya jimillar kudaden sun kamaya N‭813,408,000‬. Wanda dama miliyan 800 daga cikin biliyan 1.488 daya samu a majalissar kudaden aikin al’umma ne.

Da miliyan 13 data hau kai, zai iya bayarwa a cikin tashi gudunmawar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog