Lagos: Malami yayiwa kanwar matarshi fyade

Karatun minti 1

Da yake bayyanawa ‘yan sanda, Malam Mustapha, yace zargin da ake masa na kwanciya da kanwar matarshi sau uku ba gaskiya bane, sai dai ya amsa cewa ya kwanta da ita sau daya ne kacal.

An dai kama malamin a lokacin da yake yiwa yarinyar fyade a unguwar Bariga dake jihar Legas.

Dubun Malam Mustapha ta cika ne bayan da wasu makotan malamin suka kamashi dumu-dumu cikin yanayin aikata fyaden.

Daya daga cikin makotan ya bayyanawa manema labarai cewa, yarinyar tasha fada musu abinda Mal Mustapha yake mata, amma saboda girma da mutuncinshi yasa basa yarda.

Bayan binciken da yan sanda suka gudanar, sun tabbatar da cewa, a duk sanda mai dakin malamin ta fita, yana zagayowa domin neman kanwarta ta.

Tini dai wata kungiya mai raji kare hakkin kananan yara suka garkamashi a kotu domin fuskantar hukunci irin na doka.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa tini dai yan sandan suka tura yarinyar zuwa asibiti domin yin bincike lafiya.

Yarinyar ‘yar asalin jihar Kano ce, ‘yayarta ta kaita jihar Legas a watan Janairun 2018.

 

Karin Labarai

Latest from Blog