//
Tuesday, April 7

Malaman Firamare masu daraja sunfi Farfesoshin da sukayi aiki a zaben Kano – Kwankwaso

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa an zubar da mutuncin abubuwa dayawa a zaben Kano da aka gudanar.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da gidajen Rediyon jihar Kano.

Kwankwaso yace zaben da aka gudanar a Kano, zabe ne daya zubar da mutuncin gwamnati, jami’an tsaro dama farfesosin Najeriya, kamar yadda majiyoyinmu daga DaboFM suka rawaito.

DaboFM ta tattaro Kwankwaso yana cewa “Da farfesoshin da sukayi zaben Kano, gwara malaman firamare masu daraja.

Maganar Masarautu;

Kwankwaso yace dubu dari biyar-biyar aka bawa ‘yan majalissun jihar Kano don sun aiwatar da dokar rarraba jihar Kano.

Masu Alaƙa  Burin Shuwagabanni ne 'ya 'yan Talakawa suyi ta yi musu wahala su da jikokinsu - Kwankwaso

Kwankwaso ya kara da cewa; Sabbin Sarakunan Kano kokara suke rikewa ba sandar girma ba.”

Maganar akan neman fada a wajen Buhari;

Kwakwaso yace gwamnatin tayi amfani da kurin cewa zasu bawa shugaba Buhari kuri’u miliyan 5, sunyi ta bata masa suna a wajen shugaba Buhari, yace sunyi ta cewa Kwankwason baya son Buhari.

Kwankwason ya bada amsa da “Wayace bama son Buhari?

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020