#NigeriaDecides2019: ‘An harbe wani shugaban APC a jihar Rivers

Rahotanni sun shigo cewa wasu ‘yan bindiga da ba’asan ko suwaye su ba sun harbe wani shugaban jami’iyyar APC a jihar Rivers.

An harbe shugaba Etete tare da babban yayenshi a garinsu na Ataba dake karamar hukumar Andoni ta jihar Rivers.

Hakan ya biyo baya ne jim kadan bayan an kame wasu dage cikin shuwagabannin jami’iyyar APC tare da katinan zabe wadanda ba nasu ba kamar yadda jaridar Daily Trust suka rawaito.

Masu Alaƙa  Zaben Gwamna: Wasu fusatattun matasa sun kone mota cike da dangwalallun kuri'u a Kano

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.