Labarai Siyasa

PDP ta zargi Buhari, INEC da shirin yin magudi

Babbar jami’iyyar hammaya ta PDP ta zargi hukumar zabe ta INEC da shirya wata makarkashiya da jami’iyyar APC domin yin makudi a zaben kasar.

Shugaban jami’iyyar PDP, Mr Secondus yace, hukuncin da hukumar zabe ta yanke na dage zabe yanada alaka da shirin da shugaba Muhammadu Buhari yakeyi na sake darewa kan karagar mulkin kasar.

A lokacin da ya rage kasa da sa’o’i shida domin fara zabe a Najeriya, shugaban hukumar Prof Mahmoud Yakub ya bada sanarwa daga zaben daga 16 ga watan Fabarairu zuwa 23 ga watan.

Ko meyasa hukumar ta dage zaben?
Wasu rahotanni sun nuna cewa rashin isar kayan aikin zaben zuwa wasu juhohi, shine musabbabin dage zaben.

Za’a gudanar da zaben gwamnoni da ‘yan majalissun jiha a ranar 9 ga watan Maris.

Karin Labarai

Masu Alaka

2023: Akwai yiwuwar rugujewar APC bayan mulkin Buhari -Fayemi

Muhammad Isma’il Makama

Kai Tsaye: Sakamakon Zabe daga Birnin Kano da kewaye, Daga gidajen Rediyon Kano

Dabo Online

Zaben2019: Shugaba Buhari ya kammala kada kuri’arshi a garin Daura

Dabo Online

Zaben Gwamna: Mataimakin Ganduje ya sha kayi a akwatin gidanshi

Dabo Online

Shugaban INEC yayi murabus?

Dabo Online

Karfin wutar Lantarkin Najeriya ta ragu da 3,231MW

Dabo Online
UA-131299779-2