Labarai

Rikici ya barke tsakanin Bafarawa da Wamakko a filin jirgin sama na Sokoto

Rikici ya barke tsakanin tsoffin Gwamnonin Sokoto a filin jirgin sama na Sultan Abubakar III dake garin Sokoto wato Attahiru Bafarawa da Sanata Wamakko a ranar Litinin.

Wamakko dai shine mataimakin Bafarawa na shekara 8 lokacin yana gwamna, inda ya rubuta takardar barin aikin saboda tsoron tsigewa da yaga ana shirin yi masa a wancan lokaci.

Wamakkon ya gaje kujerar gwamna bayan yayi takara da wanda Bafarawa ya kakaba a matsayin dan takara kuma Ministan walwalar ‘Yan Sanda na yanzu, Muhammad Maigari Dingyadi.

Dabo FM ta jiyo Bafarawa yana hayaniya cewa “Ni da kace dan cirani ne a Sokoto meye na zuwa gaisheni? Ina so in gaya ma mahaifina da kakana duk a nan aka binne su zan iya nuna ma kabarinsu, kai ka nuna min na kakan ka!”

DailyTrust ta rawaito cewa shima Wamakko ya maida martani a wannan lokaci, bayan yayi kokarin gaishe da Bafarawa kuma ya auka masa da wannan maganganu.

Sanata Wamakko ya maida martani “Kaima bansan inda aka binne mahaifan ka ba, abinda na sani kawai Danchirani ne kai, kayi harkar ka in tawa!”

Daga karshe dai haka suka shiga jirgi mai zuwa Abuja tare.

Karin Labarai

Masu Alaka

Yadda dan majalisar Sokoto ya koma ga Allah bayan ya yanke jike ya fadi a majalisa

Muhammad Isma’il Makama

Sokoto: ‘Yan PDP 100,000, sun sauya sheka zuwa APC

Dabo Online

Wasu Ɓata-Gari sun guntule hannun Matashi bayan sun Kwace masa Babur a Sokoto

Dabo Online

Anyi baikon Yaro dan shekara 17, da Amaryarshi ‘yar 15 a jihar Sokoto

Dangalan Muhammad Aliyu

Sanata Wamakko zai gina katafariyar Jami’a a jihar Sokoto

Dabo Online

Ganduje na cikin jerin gwamnonin dake fuskantar barazanar tsigewa daga kotun ƙare kukan ka

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2