Tirkashi!: Wani Bakatsine ya canza sunan sa daga Buhari zuwa Sulaiman

Wani mutumin Dutsin-ma a ta jihar Kaatsina ya sanya ranar rada sabon sunan sa bayan ya canza daga Buhari zuwa Sulaiman.

Wannan ya biyo bayan abinda ya kira yaudara da matsanancin hali da yake ganin Gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari ta jefa shi dama kasar baki daya.

Buhari yace: “Bana son a ringa kira na da Buhari, saboda yaudara ta Gwamnatin Buhari.”

A wani rahoto cikin shekarar 2015 wannan taliki mai suna Buhari ya sanya wa jaririn da ya haifa suna ‘Muhammadu Buhari’, wanda shima yana shakkun canza shi.

Buhari dai ya sanya ranar Asabar 14 ga watan Disamba domin shagalin bikin sunan sa, kafin azo na jaririn sa.

Masu Alaƙa  Buhari ya aminta da a biya ma'aikata sabon albashi na N30,000 da gaggawa

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.