Nishadi

‘Yan Mata sun fara kokawa kan yadda samari sukayi ƙememe suka hana su kayan Sallah

Kamar yadda dai aka saba, mukan garzaya shafukan sada zumunta na Instagram dan zakule abubuwan dake wakana tsakanin matsan Arewa.

Yau ma mun garzaya wani shafi, inda ‘yan mata suke ta turo korafe-korafensu na cewa “Bana Samari sunyi shiru da batun kayan Sallah.”

Har ma ta kai ga kannen matan da suka amfana da kayan sallah daga samarin yayyensu suke aiko da kayayyakin da samarin suka turowa yayyen nasu domin wasu maza su gani ko sayi zuciya suma su aikawa nasu ‘yan Mata.

Binciken DaboFM ya gano wasu matan suna nuna kishinsu ga lamarin, inda suke sukar saurayin daya kawo kayan, wasu kuma suna nuna cewa ai ‘yan kayan da saurayin ya kawo ma basu kai wanda har za’a turo ayi wa nasu samarin gori ba.

Ga daga cikin martanin wadanda binciken mu ya nuna suna kishi ne don suma ba’a kawo musu ba

Daga cikin wadansu mata, su kuma sunyi kira ga mazagen da suyi kokari su kawo musu koyaya ne basai sun yi kaya dayawa ba.

kawo musu koyaya ne basai sun yi kaya dayawa ba.

Karin Labarai

Masu Alaka

An daura wa yaro dan shekara 15 aure da budurwarshi ‘yar 14 bayan yayi mata ciki

Dabo Online

Naman Sallah hakkin Iyayen Samari ne – Martanin ‘Yan mata zuwa ga Samari

Dabo Online

‘Yan Matan Arewa sun fara tallar kansu ga Mazan Aure tin bayan Auren yaro ‘dan shekara 17

Dabo Online

Jarumar barkwanci ‘yar kudancin Najeriya ta yi batanci akan Musulunci

Dabo Online

Zauren Maza da Matan Arewa a Instagram ya hada dubu dari 850 don tallafawa Jarumi Moda

Dabo Online

Ina ganin laifin Talakawa, da mutum ya samu kudi sai su yanyameshi – Aisha Falke

Dabo Online
UA-131299779-2