Matsalarmu a Yau

Sulhun shafaffu da mai a karamar hukumar Fagge

Wannan sako ne daga wani matashi daya bukaci mu boye sunanshi. Kaima zaka iya turo mana da naka sakon a shafinmu na facebook, twitter da kuma instagram.

Assalam Alaikum,

Jama’ar karamar hukumar Fagge inason inyi amfani da wannan dama domin jan hankalin wannan al’umma tamu mai albarka, musamman matasa wanda mune kashin bayan cigaban kowacce al’umma, amma sai dai bamayin amfani da hakan a matsayin abinda zai sa mu hankaltu domin samawa iyayenmu, kannenmu dama kawunanmu mafita wajen zabo abinda zai taimaka mana  wajen gudanar da rayuwarmu ta hanyar tallafa mana akan harkar ilimi, lafiya, tallafin  sana’o’i dama sauran abebadai daya kamata duk wani shugaba nagari zai kokarin nemawa al’ummarshi.

Mun san da wana ido shuwagabanninmu suke kallonmu?

Ya kai matashi, karka manta mune ake amfani damu wajen kaiwa duk wani matsayi na shugabanci wanda daga bisani ake mana anci moriyar ganga, ana amfani damu wajen cimma wata manufa musamman a lokacin siyasa, aikin zubar da jini da duk wani aiki na ba dai-dai ba a lokacin da ake sonyin haka.

Da zarar an gama wannan bukata damu, sai mu zama abin kyama, abin gudu, abin tausayi saboda anfi amfani damu bata hanyar data dace ba. Ba’a tallafa mana da sana’o’i ba, ko wani tallafin karasa karantunma ba, saidai a bamu wasu kudaden da basu taka kara sun karya ba. A wani lokaci ma akan bamu kudin da munfi karfinsu amma saboda karyewar zuciya sai mu cigaba da bin sahun su duk inda suka saka kafa muna biye dasu.

Hange na akan sulhun wakilinmu na Abuja, S.A Alibaba da Wanarabul Ata.

A duk lokacin da ake ce kakar zabe tazo, muna samun sauye-sauye dayawa a wajen wadannan bayin Allah, in zan iya tunawa an taba yin irin wannan sulhun a gabanni zaben shekarar 2015.

To me su wanarabul sukeyi nufi damu ne? Bamusan me suke nufi ba? Ko tunaninsu bai kai musu cewa zamu fahimci me suke nufi bane?

Wato muzo muyi muku wahala, ana gama zabe sai rigimarku ta kara barkewa, ku kara raba mana kawunan mu a matsayinmu na mabiyan ku. Da alama shafafffu da mai basa so muci gajiyar wahalar da mukayi muku data saka kuka dare kan madafin iko, sulhun wata shida, rigimar shekarar hudu.

Allah ya bamu ikon gano duk wata makar-kashiyar da kuke shiryawa, kuma munce baza mu yarda da wannan sulhun ba, tinda dama saboda kawunanku da iyalanku kukayi.

Wanarabul na Dandali, a baya munji kalamai dayawa wadanda suka fito daga bakinka, munga aiyuka dayawa wadanda kayi na muzanta mana tare da ‘yan uwanmu mata da ,maza, muna iya tina fitinar daka jawo mana wajen tada mana hargitsi a wajen hawan dokin kara wanda yayi sanadiyyar raunata mutanen Fagge.

Hon na Gidan Sama, muna sane da irin gurguwar goyon bayan da kake baiwa matasan da suke tare dake wajen tallafa musu na rashin cigaban karatunsu, domin akwai damar da kake da ita wajen bawa karamar hukumar Fagge tallafin Ilimi da inganta rayuwarsu akan fannin Ilimin addini dama boko.

Baba Mai Gona, muna sane da nuna halin rashin ko in kula akan yaranka da suke firta kalamai na batanci da tada tarzoma a cikin wannan al’umma tamu.

A karshe ina kira ga matasa da mu zabi chanchanta ba jami’iyya ba. Allah kuma ya bamu masu kishinmu, Allah ya zaunar mana da unguwa dama kasa baki daya lafiya.

Bissalam

Kaima zaka iya turo mana da naka sakon a shafinmu na facebook, twitter da kuma instagram, ko kuma a adreshin mu na “submit@dabofm.com”

Sako

Dabo FM batada hurumi a wannan rubtun, muna kokari domin baiwa duk wani mai kuka, damar fadin albarkacin bakinshi kamar yadda doka ta tanada

 

Karin Labarai

Masu Alaka

Arewa ta samu karuwar masu digiri na biyu sama 30 daga Jami’a daya a kasar Indiya

Dabo Online

‘Yan daba sun kai hari, gidan shugaban APC na jihar Kano

Dabo Online

Wani mutum ya kwarara wa wasu matasa 8 ruwan batir a jihar Anambra

Dabo Online

Matasa sun kone motocin APC a Abuja

Dabo Online

Matasan jihar Kano sun fara zanga-zangar kin amincewa da ƙarin masarautu 4 a jihar

Dabo Online

Ɗan gidan Tsohon Kakakin Majalissar Kano, Yusuf Ata ya makantar da wata Budurwa – Mutanen Fagge

Dabo Online
UA-131299779-2