Abba Yusuf ya kai Ganduje kotu kan ‘bai wa wasu mutane gine-ginen Gwamnati’

Karatun minti 1

Abba Kabir Yusuf, dan takarar gwamnan Kano a zaben 2019 ya mika gwamnan Kano, Dr Abdullahi Ganduje zuwa kotu tare da wasu mutane.

Lauyan dan takarar, Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzurchi ne ya sanar da haka a yau Litinin.

Ya ce sun shigar da karar ne bisa matakin da gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Ganduje ta dauka na bai wa kamfanonin Mudassir & Brothers da El Samad wuraren da suke na gwamnati domin yin kantunan zamani wanda a cewarsa wuraren na amfanin al’ummar jihar Kano ne.

Wuraren sun hada da Otal din Daula da Tashar Motoci ta Shahuci.

DABO FM ta tattara cewa sauran mutanen da dan takarar ya mika kotun sun hada da;  shugaban kamfanin Mudassir & Brothers, Alhaji Mudassir Abubakar, da shugaban kamfanin El-Samad.

Kazalika lauyan ya ce matakin da gwamnatin ta dauka na mika wa mutum guda wuraren amfanar jama’a ya saba wa muradin Talakawan jihar Kano da dokokin kasa.

DABO FM ta tattara cewar a lokacin gwamnatin jihar Kano ta shekarar 2011-2015, gwamnatin ta mayar da Otal din Daula zuwa Kwalejin Al’adu da Yawon bude ido karkashin Jami’ar Gwamantin jihar Kano dake Wudil.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog