Fadakarwa Taskar Matasa

Taskar Matasa: Tunatarwa ga Iyayenmu Mata, Daga Umar Aliyu Fagge

Ya kamata ace a kullum hankali da ilimi su ne jagorori gurin aiwatar da rayuwar mu ta yau da gobe, democradiya ta bamu damar yin za6e ne domin mu zakulo nagartattu daga cikin alumma, wanda zasu ja ragamar mu na tsahon shekaru hudu.

Hasashe ya nuna cewa mata na taka muhimmiyar rawa gurin za6o shugaba, abin tambaya a nan shi ne me Gwamnati tayi wa iyayen mu mata a baya?

Shin Gwamnati ta inganta asibitocin mu?

Wace irin kulawa ake bawa mata gurin haihuwa a asibiti?

Shin Gwamnati ta bawa mata tallafin jari domin habbaka kananan sanao’i?

Yaya makomar yayan mu maza da mata a idon Gwamnati?

Amsoshin wadannan tambayoyin a bayyane suke, an magance su ko ba a magance su ba?
Kuma muna da damar canja duk Gwnatin da ta gaza aiwatar da wadancan aikace-aikacen da da na zayyano.
Kada wata a cikin iyayen mu mata ta bari ayi amfani da naira dubu daya N1000 ko atamfa gurin siyan ra’ayin ta, dubu daya baza tayi miki maganin matsalolin rayuwar da zaki fuskanta ba a shekaru hudu.

Zaku iya aiko mana da rubutu akan wani maudu’in kawo gyara a cikin al’umma ta email  dinmu “[email protected]

UA-131299779-2