Kotu ta sake dakatar da Ganduje akan kirkirar sabuwar Majalissar Sarkunan Kano

Wata babbar kotu a jihar Kano wacce mai shari’a A.T Badamasi yake jagoranta ta dakatar da gwamnatin jihar Kano daga wanzar da kirkirar sabuwar Majlissar Sarakunan jihar Kano.

A cikin makon nan ne dai gwamnan jihar Kano ya sanya hannu a sabuwar dokar da Majalissar dokikin jihar Kano ta amince da ita domin kirkirar Sarakuna 4 da sabuwar Majalissar jihar Kano.

Sabuwar Majalissar zata kunshi sabbin Sarakuna 5 na jihar Kano, Bichi, Gaya, Kano, Karaye da Rano. Haka zalika zata kunshi masu nadin Sarki guda 10 (2 daga kowacce Masarauta) kwamishinan kananan hukumomi, shuwagabannin kananan hukumomi 5 inda Sarakunan suke, Sakataren gwamnati da jami’an tsaro da ‘yan Kasuwa.

Rahotanni sun bayyana cewa masu zabar sarki a masarautar Kano wanda suka hada da Madakin Kano Yusuf Nabahani da Makaman Kano Abdullahi Sarki Ibrahim da sarkin Dawaki mai tuta Bello Abubakar da kuma Sarkin Bai Mukhtar Adnan ne sune suka shigar da karar suna kalubalantar kafa majalisar ta sarakunan jihar Kano.

Masu Alaƙa  Yanzu-Yanzu: Jiga-jigen APC sun dira a Habuja da duku-duku kan shari'ar zaben Kano

Kotun dai ta dakatar da Kirkirar sabuwar Majalissar tare da ayyana ranar 17 ga Disamba domin fara sauraren karar.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.