Wasu ‘yan bindiga sun sace wani farin fata, sun kashe 1 a Kano

A safiyar yau talata a birni Kano wasu ‘yan bindiga suka sace wani farar fata tare da bindige direban motarshi.

Farar fatar da yake aiki a kamfanin Trichia Constructions, kamfanin da ke aikin gadar kasar da gwamnatin jihar keyi a titin Gidan Zoo.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, wani mai shedar gani da ido, wanda ya bukaci a sakada sunanshi yace, al’amarin ya faru ne a yau da misalin karfe 7 na safe bayan dawowar ma’aikatan daga hutu bayan kammala zabe.

“‘Yan bindigar na zuwa wajen aiki ne dai suka harbe direbanshi kafin sun dauke wannan farar fatar.”

Da yake jawabi, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi ya tabbatar da faruwar al’amarin tare da bayyana wannan farar fatar da aka sace a matsayin dan kasar Lebanon.

Masu Alaƙa  Satar yara a Kano: Fiya da yara 38 yan kasa da shekaru 3 aka sace a karamar hukumar Nassarawa

Haruna, da zarar hukumar ta gama gudanar da bincike zata nema kafafen yada labarai domim bayyana yadda ake ciki.

 

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.