Kano: Zaben gwamnan jihar Kano yana da gibi, za’a tafi zagaye na biyu

Jami’iyyar PDP na kan gaba tare da rinjayen kuri’u 1,014,474 yayin da jami’iyyar APC ta samu 987,819.

Sai dai adadin kuri’un da aka soke, sunfi adadin yawan tazarar kuri’un da take tsakanin jami’iyyar da take jan ragama tare da wacce take ja mata baya.

Jami’iyyar PDP tace bata yadda da wannan sakamakon da lamari ba musamman wajen soke wata mazaba da ake zargin wasu jami’an gwamnati da zuwa domin tada hargitsi tare da yaga takardar tattara sakamakon zaben.

Yanzu dai wakilin jami’iyyar ta PDP yaki saka hannu akan takardar sakamakon da hukumar ta fitar, bisa rashin amsar tambayar da yayiwa baturen zaben akan soke zaben wasu mazabu.

Masu Alaƙa  Kano: Mutane 176 ne suka rasa ransu sakamakon hadarin jirgin sama a rana irin ta yau

Sauran labari na zuwa….

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.