Gwamnatin Kano nayin duk mai yiwuwa domin a chanza CP Wakili

Karatun minti 1

Duba da irin abubuwan da suka faru a zaben da ya gudana na gwamnoni da ‘yan majalissun jiya a ranar Asabar 9 ga watan Maris 2019, gwamnanatin jihar Kano ta kai kuka domin ganin an chanza kwamishinan yan sanda, CP Muhammd Wakili.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito, wasu majiyoyin sirri sun bayyanawa wakilanta cewa gwamnan jihar Dr Abdullahi Ganduje tare da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar suna babban birnin tarayyar Abuja domin rokon shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya, IGP Ibrahim Idris, yayiwa CP Muhammad Wakili chanjin gurin aiki.

“Daga cikin masu goyon bayan chanzi sun hada da, shugaban jami’iyyar APC na kasa, Ahmad Oshiomole, Bola Ahmad Tinubu da wasu daga cikin manyan jiga-jigan gwamnatin tarayya.” -Kamar yadda jaridar ta Daily Nigerian ta rawaito.

A zaben daya gabata dai, kwamishinan yan sandan na jihar Kano, Wakili ya taka rawar gani wajen dakile tada hargitsi tare da yunkurin yin magudi a lotunan zaben.

Lamarin da ya kai kwamishinan da damke mataimakin gwamnan jihar Kano, Dr Nasiru Yusuf Gawuna, kwamishan kananan hukumomi, Murtala Sulen Garo, hadi da shugaban karamar hukumar Nassarawa.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Latest from Blog