Siyasa

‘Yan Kwankwasiyya sun dauki hanyar kawo wa Shari’ar ‘Abba Gida-Gida’ cikas

Matsalar barazana da cin mutunci da akayi wa Wakiliyar INEC wacce lauyan INEC ya shigar da kokensu gaban Kotun zaben Kano, za ta iya bude wani shafin Shari’ar na daban wanda haka na iya baiwa PDP cikas.

Ranar Laraba ne dai lauyan INEC, Barista Adedeji ya bayyanawa kotu cewa; “An kai wa shaidar da hukumar INEC ta gabatar hari irin na Sojojin bakar kafafen sada zumunta.”

Lauyan ya kara da cewa ana alakanta jami’ar INEC da yiwa gwamnatin jihar Kano aiki tare da ci mata zagin kare dangi da cin mutunci ta hanyar saka hotunanta da fadar maganar cin zarafi.

Duk da Lauyan INEC bai fadi wadanda suka aikata hakan ba, DABO FM ta bincika kafafen sada zumuntar domin gano wadanda suka ciwa jami’ar INEC din zarafi.

DABO FM ta gano wani shafi mai sunan “Kwankwasiyya Reporters” a kafar Facebook, inda suka rubuta kalamai wadanda suka sabawa dokar kasa akan jami’ar INEC din.

WANNAN MA’AIKACIYAR INEC CE ME SUNA HALIMA DA TACE ANYI ZABE GWAMNA ZAGAYE NA BIYU LAFIYA A MAZABAR GAMA DAKE KARAMAR…
Posted by Kwankwasiyya Reporters on Tuesday, August 20, 2019Karin Labarai

Masu Alaka

Dama can nasan Ganduje ne yaci zaben Kano -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

Kotu ta kwace kujerar Majalissar Tarayya, ta baiwa PDP

Dabo Online

Shari’ar Abba da Ganduje tana neman baiwa ‘Yan Kwankwasiyya mamaki, INEC ta nemi a kori karar

Dabo Online

Kotun Zabe: Na shiga tsananin ruɗani a lokacin da kotu take yanke hukunci – Buhari

Dabo Online

Kotu ta kori karar Abba Kabir Yusuf, ta tabbatar da Ganduje

Dangalan Muhammad Aliyu

Kotun Koli ta karbe kujerar gwamna daga PDP ta bawa APC mai mulki

Dabo Online
UA-131299779-2