Zamfara zata fara noman kwakwar man ja – Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, yace jihar zata tsunduma cikin harkokin noma nan bada dadewa ba, musamman na kwakwar manja domin fara samar da manja a jihar.

Ranar Alhamis, a garin Gusau, Gwamnan ya bayyanawa manema labarai cewa gwamnatin zata bukasa harkokin noma a jihar kuma zatafi bada hankalinta wajen fara samar da man ja a jihar.

“Zamu nemi masu zuba jari daga kasashen waje domin fara samar da manja a Zamfara.”

“Zamu kawo sauye sauye a bangaren noman domin mayar da bangaren mai alfanu.”

“Zamu zuba jari sosai a bangaren domin farfado da kauyuka da suka rasa samun alfanu da kwanciyar hankali daga irin matsalar rashin tsaro da ya hanasu zuwa gonakinsu.

“Gwamnatin zata kuma gyara shirin ban ruwan Bakalori domin ingantanta harkokin noma a kasar. Zamu kuma kawo tsare tsare wanda zasu samar wa da masana’antun mu wutar lantarki.”

%d bloggers like this: