Yanzu-yanzu: An Gwabza da ‘Yan Shi’a da Jami’an Tsaro

Labarin Da Ke Shigo Mana Yanzu Na Nuna Cewa Yan Kungiyar Shi’a Ta Imn Sun Cika Alkawarinsu A Yau Talata Na Gudanar Da Muzaharar Ranar Ashura Duk Da Gargadin Hukumar Yan Sandan Najeriya.

Yan kungiyar sun taru a kasuwar Wuse dake birnin tarayya Abuja misalin karfe 7 na safe kuma suka nufi shataletaken Berger.

Yan Shi’an sun watse a Abuja yayinda suka ga yan sanda sun nufo wajensu. Wannan abu ya kawo cinkoso a titunan gari.

A yanzu haka, an rufe manyan titunan Kubwa da Mararaba.

Hakazalia rahotanni daga jihar Kaduna na nuna cewa rikici yan barke tsakanin yan Shi’an da yan sanda a garin Kaduna inda kawo yanzu an bindige mutane uku. Sahara Reporters ta ruwaito.

Masu Alaƙa  Turmutsutsu ya hallaka 'Yan Shia 31, ya jikkata 100 a birnin Karbala na kasar Iraqi

Wasu da dama sun jikkata.

Wani mazaunin Kaduna, Abdu na Abdu ya Shaidawa jaridar Legit.Hausa cewa da sassafe sun ji harbe-harbe a babban titin Nnamdi Azikwe na jihar Kaduna

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: