Home Kiwon LafiyaYaro mai shekara 5 ya kamu da Kwabid-19 a jihar Niger

Yaro mai shekara 5 ya kamu da Kwabid-19 a jihar Niger

by Dabo Online
0 comments

Rahotanni sun tabbatar da wani yaro mai shekara 5 kacal a duniya da ya kamu da cutar Kwabid-19 a jihar Niger.

Yaron da yake a karamar hukumar Chanchaga yana daga cikin mutum 13 da suka kamu rana daya a jihar.

Hakazalika matasa ‘yan rukunin shekaru 20 guda 3 suna cikin wadanda suka harbu da cutar a jiya Alhamis, ranar da cutar ta fi kama mutane a jihar.

Cikin wata sanarwa da kwamitin yaki da cutar a jihar Niger ya fitar, kwamitin ya bayyana cewa jumullar mutum 79 ne aka tabbatar da suna dauke da cutar Kwabid-19 a jihar.

Kwamitin yace an samu mutane 13 na ranar Alhamis a karamar hukumar Chanchaga baki daya, yayin da biyar daga cikinsu mata ne.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00