1
Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa an zubar da mutuncin abubuwa dayawa a zaben Kano da aka gudanar.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da gidajen Rediyon jihar Kano, kamar yadda majiyoyin DaboFM suka tabbatar.
Kwankwaso yace zaben da aka gudanar a Kano, zabe ne daya zubar da mutuncin gwamnati, jami’an tsaro dama farfesosin Najeriya.
DaboFM ta tattaro Kwankwaso yana cewa “Da farfesoshin da sukayi zaben Kano, gwara malaman firamare masu daraja.
