A daidai lokacin sabbin gwamnoni ke neman kwanaki 100 a ofis, 18 daga cikin Gwamnoni 29 har kawo yanzu ba su nada mukaman masu taimaka musu ba.
DABO FM ta binciko jerin Gwamnonin da basu nada mukamai ba kamar jihohin
Jigawa, Ogun, Abia, Kebbi, Taraba, Zamfara, Kwara, Yobe, Gombe, Adamawa, Kano, Niger, Cross River, Enugu, Katsina, Plateau, da kuma Ribas.
Zuwa yanzu, gwamnoni 12 ne suka nada tare da rantsar da mukarabbansu wanda ake sa ran yin bikin kwanakinsu 100 da kama aiki.
Jihohin sun hada da; Akwa Ibom,Bauchi, Binuwai, Borno, Ebonyi, Delta, Imo, Kaduna da Lagos, Jigawa.
A jihar Jigawa, Gwamna Badaru har kawo Yanzu bai fadi mukarrababsa ba, in ban da Sakataren Gwamnatin jiha, sannan har kawo lokacin da nake hada wannan rahoto, babu ko da alamun hakan. Gwamnan yana aiki ne da mataimakinsa da kuma sakatarorin dindindin na ma’aikatun Jihar. Majiyar mu ta tabbatar da cewa Gwamnan dai, baya zaman Jihar na sati Biyu, yana yawan tafiye-tafiye.
A Jihar Kano kuma, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya nada wasu mukaman da dama, bayan zabarsa a karo na Biyu, amma shi ma, bai nada kwamashinoni ba har kawo Yanzu.
Da yake zantawa da Jaridar Daily trust, kakakin Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar, yace Jan kafar da aka ga suna yi, ana yi ne, don a zakulu hazikan mataimaka.
