Home Labarai‘Yan Sanda sun samu nasarar bundige Iblis a Najeriya

‘Yan Sanda sun samu nasarar bundige Iblis a Najeriya

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Iblis dai wani hatsabibin mai garkuwa da mutane ne dake jihar Ribas, inda rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Ribas a ranar Litinin suka samu nasarar kashe wannan gawurtaccen mai garkuwa da mutane mai suna Ekweme Brown da ake yi wa lakabi da Lucifer ma’ana ‘Iblis’.

Lucifer dan asalin kauyen Egamini Rundele ne a karamar hukumar Emohua da ke jihar Rivers.

Jami’an ‘yan sandan Operation STING karkashin jagorancin kwamandansu, ACP Shem Evans ne su kayi nasarar halaka Lucifer kamar yadda Linda Ikeji Blog ya ruwaito.

Ana zargin cewa shugaban na kungiyar miyagun yana da hannu cikin mafi yawancin garkuwa da mutane da tare matafiya da ake yi a hanyar Ndele na East/West Road. Gabadaya al’ummar Rundele suna ta farin ciki bayan samun labarin mutuwar hatsabibin mai garkuwa da mutanen.

Rundunar ‘yan sandan ta ce ana cigaba da bincike domin kamo sauran ‘yan tawagarsa domin su fuskanci shari’a.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00