Home LabaraiYanzu-Yanzu: An faɗi gabana ana rokon tilas saina tumɓuke rawanin Sarki Sanusi -Ganduje

Yanzu-Yanzu: An faɗi gabana ana rokon tilas saina tumɓuke rawanin Sarki Sanusi -Ganduje

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa a yau alhamis gamayyar kungiyoyi fiye da 35 sunyi kira da ya tsige Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ba tare da bata lokaci ba.

Rahoton mu na Dabo FM ya rawaito mai magana da yawun gwamnan, Malam Abba Anwar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikewa da PremiumTimes.

Anwar yace “Gamayyar kungiyoyin sunyi kiran ne bayan da suka bayyana Sanusi da cewa yana kokarin ya kafa wata jihar a cikin jihar Kano.”

Kamar yadda shugaban gamayyar kungiyoyin ya rattaba hannu kan takardar da suka aikewa gwamna Ganduje.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00