Rahotanni sun tabbatar da jami’ar Ahmadu Bello ta bawa Alkalin alkalai, CJN Tanko Muhammed gurbin karatu ba tare da ya samu makin da ake bukata ba a darasin Lissafi da Turanci.
Rahoton Dabo FM ya bayyana wannan yazo ne cikin takardun sakamakon CJN Tanko wanda ya nuna yana da makin ‘Credit’ 3 da ‘Pass’ 2, kamar yadda jaridar DailyTimeTV ta fitar.
Kamar yadda sakamakon jarabawar sa ta yammacin Afirka, WAEC ta nuna, wadda Jastis Tanko ya zauna a 1973, Jastis ya samu makin ‘C5’ a Darasin Hausa, kana ‘C4’ a Darasin Tarihi da ‘C6’ a Darasin Ilimin Addini (IRK).
Haka kuma ya samu makin ‘Pass’ a ilimin kimiyya wato Kemistire da Darasin koyon harshen Larabci. Duba hotuna a kasa..