Home LabaraiKwankwaso ya roki jami’an tsaro na farin kaya su nemo inda Dadiyata yake

Kwankwaso ya roki jami’an tsaro na farin kaya su nemo inda Dadiyata yake

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments
Abubakar Idris Dadiyata

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bukaci hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS, da ta zurfafa bincike don gano matashin nan Abubakar Idris Dadiyata, wanda ya yi batan dabo bayan wasu mutane da ake zargi jami’an tsaro ne sun dauke shi daga gidansa.

Rahoton Dabo FM ya tattara cewa a ranar 1 ga watan Agustan 2019 ne da daddare aka je har gidansa da ke Kaduna aka dauke Dadiyata, wanda ya yi fice a shafukan sada zumunta wajen sukar gwamnatin jam’iyyar APC mai mulkin kasar.

Dadiyata ya kuma yi suna wajen goyon bayan kungiyar siyasa ta Kwankwasiyya, wadda tsohon gwamnan Kano Kwankwaso ya assasa.

A wata hira da ya yi da ‘yan jarida a gidansa da ke Kano a ranar Alhamis da daddare, Sanata Kwankwaso ya ce batan Dadiyata abin damuwa ne matuka.

Ya ce ya kamata hukumomin da abin ya shafa su yi kokarin gano Dadiyata, wanda malamin jami’a ne a kasar, inda ya ce “muna fatan Allah ya bayyana shi cikin lokaci mafi kankanta.”

“Muna nan muna ci gaba da tausayawa da jajanta wa iyayensa da iyalinsa da abokansa da dukkanin mutanen da suka shafe shi,” in ji Kwankwaso. Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00