Home LabaraiZamu fara amfani da gogewar mu ta yakin Basasa domin fatattakar Boko Haram -Buhari

Zamu fara amfani da gogewar mu ta yakin Basasa domin fatattakar Boko Haram -Buhari

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sojojin Najeriya nada kwarewar da zasu fatattaki Boko Haram a arewa maso gabas.

Majiyar Dabo FM ta bayyana cewa Buhari yayi wannan batu ne a Habuja ranar Juma’a, inda yace “Da gogewar da sojojin Najeriya suke da ita ta watanni 30 na yakin Basasa zasu fatattaki ta’addancin Boko Haram wanda ya addabin arewa masu gabas a fadin Najeriya.”

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne sa’ilin da kwamishinan kungiyar tarayyar turai bangaren tashe tashen hankula, Janez Lenarcic ya ziyarce shi a gidan gwamnatin Najeriya.

A kwanakin kadan da suka shude dai mun kawo muku rahoton kungiyar tarayyar turar, ‘European Union’ wanda tayi tir da kashe-kashen tare da fadin ita fa bama ta ga wani canji wajen yaki da Boko Haram ba.

Cikin yan kwanakin nan dai hare haren kungiyar Boko Haram yayi tsamari inda har ta kai ga mutuwar mutane bila adadin, ciki harda shugaban kungiyar kiristoci ta Adamawa tare da wani dalibi da faifan bidiyon sa ya yadu.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00