Wasu mahara sun bude wa motoci wuta a babban birnin tarayyar Najeriya dake Abuja, kana sunyi gaba da fasinjoji da dama.
Majiyar Dabo FM ta ruwaito cewa kakakin rundunar yan sanda ta Abuja, Anjuguri Manzahshine ya bayyana hakan, yace yan bindigan sun kai wannan hari ne a ranar Lahadi 2 ga Fabureru, misalin karfe 17:30 kan babban titin Piri Kwali.
Wannan hari ya zo ne bayan sace wani dalibi kimanin sati daya daya gabata cikin babban birnin tarayyar, da yake tabbatar da faruwar hakan, Anjuguri Manzah ya kara da cewa hukumar yan sanda ta yi kokarin tseratar da wasu saidai yan bindigar sun samu nasarar tserewa da fasinjoji.
Kakakin yan sandan ya kuma bayyana hukumar tayi nasarar damke mutane 4 wanda ake zargi.
