2
Jami’iyyar PDP da wasu jami’iyyu a Najeriya ba su aike da sunan kowane ɗan takara da zai yi musu takarar shugabancin Najeriya ba.
Sauran jami’iyyun sun haɗa da APGA da kuma Labour Party, kamar yadda wani babban ma’aikacin hukumar INEC ya shaidawa Daily Trust.
Ya ce kusan dukkanin jami’iyyun siyasa a Najeriya sun gama shigar da sunayen ‘yan takarkarunsu a shafin da hukumar ta ware.
“Zuwa yanzu, jami’iyyu 3 ne kadai ba su gama shigar da sunayen ƴan takarkarunsu na shugabancin ƙasa ba na zaɓen shekarar 2026.
