Labarai

Aisha Buhari ta yiwa Mamman Daura da Garba Shehu kaca-kaca a Villa

Tun a cikin watan Oktoba ne tsamin dangantaka ya tsananta tsakanin iyalan Mamman Daura da A’isha Buhari bayan ta dawo daga balaguron watanni biyu daga Turai.

Wani faifan bidiyo da aka yada a shafun sada zumunta a kwanakin baya, ya nuna yadda uwargidan shugaban ke tayar da jijiyoyin wuya a gaban ‘yar Mamman Daura, wato Fatima saboda kulle wata kofa a fadar shugaban kasa.

A wata wasika da ta sanya wa hannu da kanta wadda kuma ta aika wa Jaridar Daily Trust a wannan Larabar, A’isha ta ce, Mamman Daura ne ya bayar da umarnin soke ofishin ‘matar shugaban kasa’ inda ya yi amfani da Garba Shehu, mai magana da yawun fadar wajen yayata wannan umarnin.

A rahoton Dabo FM daga ‘rfi’, A’isha tace: “Garba Shehu ya wuce gona da iri” tana mai cewa, umarnin ya tozarta shugaba Muhammadu Buhari.

A’siha ta zargi Shehu da kauce wa gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansa, yayin da ya karkata hankalinsa wajen hidimta wa wani bangare da ta ce, yana amfani da shi wajen cimma miyagun manufofinsa.

Uwargidan ta ce, kamata Garba Shehu ya yi murabus cikin gaggawa saboda ya wuce iyakarsa.

Karin Labarai

Masu Alaka

Buhari ya dawo Najeriya bayan shafe kwanaki 10 a kasar Birtaniya

Dabo Online

Buhari ya dora alhakin hare-haren kisan kiyashi na ‘yan ta’adda a Arewa kan annobar Korona

Muhammad Isma’il Makama

Nan gaba duk dan takarar shugaban kasar da yazo yana muku kuka to kuyi ta kanku -Shehu Sani

Muhammad Isma’il Makama

Buhari ya dakatar da dukkanin Jami’an Gwamnati daga fita kasashen Waje

Dabo Online

‘Yan Najeriya sun yanke hukunci, NNPC ta huta?, Buhari yaci zabe.

Dangalan Muhammad Aliyu

An zabi Buhari a matsayin shugaban Najeriya mafi muni a tafiyar da mulki cikin shekaru 20

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2