Labarai

APC ta dakatar da Hon Abdulmumin Jibrin Kofa bisa cin amanar Jami’iyya

Jami’iyyar APC reshen karamar hukumar Bebeji ta jihar Kano ta dakatar da dan majalissar tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji, Hon Abdulmumin Jibrin (Kofa Maliya)

DABO FM ta tabbatar da cewa; APC ta bayyana cewa ta kama Hon Kofa da laifin yiwa jami’iyyar zagon kasa tare da sabawa wasu dokokin jami’iyyar.

Jami’iyyar ta kama Hon Kofa da aikata abubuwa wadanda suka ci karo da dokar ta 21, babin A(ii),(v), (vii), da xi).

Ta kara da cewa bisa zama da kwamitin zartarwa na jami’iyyar ya gudanar, sun yanke hukuncin dakatar da shi har na tsawon watanni 12.

DABO FM ta binciko cewa; akwai alamu rashin jituwar Hon Abdulmumin da shugaban Jami’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas.

A baya an jiyo Hon Kofa yana cewa dukkanin wani tashin hankali ko aikata wani lamari mara dadi a jihar Kano, Abdullahi Abbas ne sila ko shine yake hura wuta baya so a daina.

Hakan yasa jami’iyyar ta kori duk wasu wadanda aka sansu a matsayin masu bin tafiyar Kofa a karamar hukumar Kiru da Bebeji.

Karin Labarai

Masu Alaka

‘Yan daba sun kai hari, gidan shugaban APC na jihar Kano

Dabo Online

Mawaƙan ‘Buhari Jirgin Yawo’ sun ga ta kansu a hannun wani ɗan siyasa

Muhammad Isma’il Makama

2023: Akwai yiwuwar rugujewar APC bayan mulkin Buhari -Fayemi

Muhammad Isma’il Makama

Bayan durkuso da gaisuwar bangirma, alamu sun nuna APC tayi wa Hon Kofa ‘Anti Party’

Dabo Online

Taraba: Yawon kamfen a jirgin kwale-kwale

Dabo Online

Mun sa Kwankwaso ya ajiye siyasa da karfin tuwo – Ganduje

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2