Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Rikici ya barke a taron Atiku na jihar Legas

1 min read

Wasu matasa sun tada hargitsi a taron da jami’iyyar PDP tare da dan takarar shugaban kasar ta Alhaji Atiku Abubakar suke gudanarwa a jihar Legas.

Tin kafin zuwan Atiku filin taron na Abubakar Tafawa Square, an shaidawa jami’an tsaro cewa akwai matasa da suka zo domin su tada hargitsi.

Matasan sunyi ta jifan junansu da kujeru da sauran abubuwan da ka iya illata ‘dan adam.

Tini dai jami’an tsaro suka shigo domin awon gaba da bata garin matasan.

Kwana hudu ya rage a gudanar da babban zabe, yan siyasa ta kowacce fuska guna bi lungu da sako domin tallatawa al’umma manufofinsu.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.