Kaduna: Hatsari ya ritsa da wasu matasa a wajen murnar cin zaben Shugaba Buhari

A saifyar yau, al’ummar Najeriya magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari suka fito domin nuna murnar lashe zaben da yayi a zaben da gudanar asabar din data wuce.

Sai dai labarai suna zuwa marasa dadi ta yacce matasa suke murna ta hanyar wasa da ababan sufuri da suka hadar da motoci da kuma babura , abinda takai anji raunuka dama asarar rayuwa a jihar Kaduna.

Anyi ta kira ga matasa da su nuna murnarsu ta hanyar data dace batare anyi barna ko asarar rai ba, shima SWhugaba Muhammadu Buhari yayi wannan furuci a jawabinshi na nuna godiya ga wadanda suka zabeshi dama ‘yan Najeriya baki daya.

Masu Alaƙa  Kano: Zaben gwamnan jihar Kano yana da gibi, za'a tafi zagaye na biyu

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.