Siyasa

Munada Shugaban Ƙasa, ‘Yan sanda da Sojoji, ko PDP taci zaɓen Gwamna sai mun ƙwace – Abdullahi Abbas

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas yayi wasu kausasan kalamai akan abokin hamayyarsu, tsohon gwamnan jihar Kano Engr Rabi’u Kwankwaso tare da dan takarar gwamnan jihar kano karkashin inuwar jami’yyar PDP,  Abba Kabir Yusuf.

Abdullahi Abbas yace bazasu ragawa madugun darikar Kwankwasiyyar ba, kuma zasuyi duk abinda zasuyi domin ganin sun kaishi kasa.

Yayi kira da magoya bayan Dr Abdullahi Umar Ganduje da su ci mutuncin duk wani dan Kwankwasiyya a jihar Kano domin su ba mutane bane wadanda za’ayiwa mutunci, kamar yadda shugaban APC  Abddullahi Abbas ya fada.

“Ranar Zabe, sai anyi kare jini, Biri jini, mun fada musu ko da tsiya, ko da tsinya tsiya mu zamuci mulki a Kano, abinda muka yadda, da’a kwacewa Yaro Riga, gwara a yaga ta.”

“Mun fadawa Kwankwaso mu zamuci zabe a Kano, ko yana so ko baya so.”

“Mu kada su zabe, inda ma sukaci mu kwace, munada  shugaban Kasa, munada ‘yan sanda, munada soja, munada dan sarki. Kuma bayan mun kadasu zamuyi musu duka.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Duk wata rigima da akeyi a Kano akwai hannun Abdullahi Abbas a ciki – Hon Abdulmumin Jibrin

Dabo Online

Zaben2019: Ko a lahira ba abinda za’ayi idan mukaci zabe da tsiya-tsiya a Kano – Shugaban APC

Dangalan Muhammad Aliyu

Ganin sabon dan majalisar PDP da ya kayar da Kofa tare da shugaban APC ya jawo cece-kuce

Muhammad Isma’il Makama

Kofa ya tsugunna mana har kasa don mu roki mutane su zabe shi amma suka ki – Abbas

Dabo Online
UA-131299779-2