//
Thursday, April 2

Zaben Gwamnoni: Zan karɓi kayi idan na fadi zabe – Ganduje

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje yace da zarar alkaluma sun nuna wanda zaiyi nasara a zaben gwamnoni da za’a gudanar ranar Asabar, nan take bada wani bata lokaci ba zai kirawo wanda yayi nasara yayi masa murnar lashe zaben.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen wata ‘yar ganawa da yayi da manema labarai bayan kammala taron kulla yarjejeniyar zaman lafiya a jihar Kano a lokacin zabe dama bayan zaben.

“A shirye nake da mika wuya ga sakamakon zabe, domin nasan mulki na Allah ne kuma shi ke yin komai a duk sanda yaso. Duk wanda ya samu nasara, take zan dauko waya in buga masa domin nayi masa murnar lashe zabe.”

Masu Alaƙa  Zaben Gwamna: Jami'an tsaro sun damke wata mota dankare da kudade a Sokoto

Taron kulla yarjejeniyar zaman lafiyar da aka gudanar jiya a Kano, ya samu halartar Mai martaba Sarkin Kano, Mallam Muhammad Sunusi II, manyan malaman addini Islama, Kiristanci, hadi da masu takarar gwamna sama da 30 ciki harda babban abokin hamayya, Engr Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP.

Kwanaki kasa da uku ne suka rage a gudana da zaben gwamnoni da ‘yan majalissun jiha a fadin tarayyar Najeriya, wanda za’ayi 9 ga watan Maris shekarar 2019

Karin Labarai

Share.

About Author

•Sublime of Fagge's origin. •PR Specialist •PharmD candidate

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020