Siyasa

Sokoto: ‘Yan PDP 100,000, sun sauya sheka zuwa APC

Jami’iyyar APC a jihar Sokoto tace ta karbi ‘yayan jami’yyar PDP da SDP wadanda suka fito daga kananan hukumomi 23 a jihar ta Sokoto.

Mai tamakawa shugaban jam’iyyar a kafafun sadarwa na jami’iyyar a Sokoto, Malam Bashir Mani, yace masu sauka shekar sun samu tarba a wajen Sanata Wamako a yayin gudanar da taron yakin neman zabe a arewacin jihar.

“Munji dadin wannan tunani da kukayi na dawowa wannan jami’iyya mai albarka, kuma hakan yana nuna mana cewa dan takararmu zai samu nasara, domin mutun ne mai kwazo wanda zai dawo da martabar jihar Sokoto.” – Sen Wamako

“A muhawarar da aka tafka ma, ina fatan mutane zasu gane cewa dan takararmu, Alhaji Ahmed Aliyu a shirye yake domin karbar aiki”.

Daga karshe sanatan yayi kira da su tabbata sun zabi shugaba Muhammadu Buhari domin cigaba da kyawawan aiyuka da yakeyi a jihar dama kasa baki daya.

Gobe Asabar, 16 ga watan Fabarairu, rana ce da za’a gudanar da zaben kasar Najeriya, matakin Shugaban kasa, yan majalisar dattijai tare da ‘yan majalisar wakilai.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kano Municipal: APC batada ‘dan takarar majalisar tarayya – INEC

Dabo Online

Kotun koli ta kwace zaben dan majalissar tarayya na APC a jihar Adamawa

Dabo Online

Babu dan PDP ko daya da zai rike mukami a shugabancin Majalissar Tarayya – Oshiomole

Dabo Online

2023: Akwai yiwuwar rugujewar APC bayan mulkin Buhari -Fayemi

Muhammad Isma’il Makama

Kotun ‘Allah-ya-isa’ ta fatattaki Akitu tun ba’a je ko ina ba

Muhammad Isma’il Makama

APC ta shirya korar Abdul’aziz Yari daga jami’iyyar

Dabo Online
UA-131299779-2