Jami’iyyar PDP ta lashe dukkanin kujerun mulki a jihar Zamfara a karon farko tin kafa jamhuriyya a Najeriya.
PDP ta lashe dukkanin kujerun majalissar jiha guda 23. Sanatoci 3 da majalissar wakilai 7.
Jami’iyyar NRM ta lashe dan majalissar jiha guda 1 mai wakilatar Maru ta Kudu.
Hakan na zuwa ne bayan da Kotu koli ta kwace nasarar da jami’iyyar APC tayi bisa rashin gudanar da zaben fidda gwani a jami’iyyar.
Kotu tace dukkanin kuri’un da APC ta samu ya tashi a iska, inda tace a baiwa dukkanin jam’iyya da dan takarar dake biyewa APC baya a yawan kuri’u.
Hakan ne ya tabbatar da dan takarar gwamna na jami’iyyar PDP, Bello Matawalle a matsayin zababben gwamnan jihar tare da ‘yan majalissun jiha, tarayya da sanatoci.
