‘Yan Majalissar jiha guda 6 a jihar Imo sun sauya sheka zuwa PDP

‘Yan Majalissar jiha guda 6 a jihar Imo sun sauya sheka zuwa jami’iyyar PDP a yau Litinin.

Yan majalissar sun bayyana chanzin shekartasu a wata takarda da suka mikawa kakakin majalissar jihar wacce ta samu karatu daga magatakardar majalissar.

Yan majalissar wadanda asalinsu yan jami’iyyar AA ne sun hada da Mike Iheanaetu (Aboh Mbaise), Victor Onyewuchi (Owerri ta Yamma), Ken Agbim (Ahiazu Mbaise) Lloyd Chukwuemeka (Owerri ta Arewa) da Bruno Ukoha (Ezinihittte Mbaise)

Chiji Collins (Isiala Mbano) ya sauya daga APGA zuwa PDP.

Masu Alaƙa  Sokoto: 'Yan PDP 100,000, sun sauya sheka zuwa APC

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.