ZABEN KANO: Duk wanda yace anyi kisa a zaben Kano, ya kawo Hujja – Gwamnatin Kano

Karatun minti 1

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Dr Abdullahi Ganduje ta musanta zarge-zarge da akeyi mata na samun hargitsi wanda har yayi sanadiyyar asarar rayuka sama da guda 5 a lokacin da aka gudanar da cike zaben Gwamna a jihar ta Kano ranar 23/03/19.

Da yake bayani yau a taron manema labarai, Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba ya ce babu wani abu mai suna tada hankali a zaben da aka gudanar a jihar Kano.

Gwamnatin ta kalubalanci duk mai cewa anyi kisa ya kawo hujjar da zata tabbatar da haka.

“Babu wanda ya fito yayi zanga-zanga a jihar Kano bayan an bayyana sakamakon zabe a jihar Kano.”

Ranar zaben dai hotuna sukayi ta yawo a shafukan sada zumunta dama wasu manyan Jaridun Najeriya, sun nuna yadda akayi amfani da wasu matasa, majiya karfi tare da mugayen makamai wajen hana mutane yin zabe cikin nutsuwa.

Wasu majiyoyin sun rawaito cewa matasan har  duka suke yiwa wadanda suka zo zaben wata jami’iyya wacce su ‘yan daban ba ita suke yi ba.

An samu bidiyoyi dayawa wadanda mata suke korafin cewa an musu tsirara domin sunzo zabar wata jami’iyya ta daban, duba da yadda akace ‘yan daban sun mamaye akwatinan zaben.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog