Zaben Kano: Takai bai ce azabi Ganduje ba – Yasir Ramadan

Yasir Ramadan Gwale, dan gwagwarmaya kuma halastaccen mabiyin Mallam Salihu Sagir Takai, dan takarar gwamnan Kano a  jami’iyyar PRP, yace Takai bai umarci magoya bayanshi su marawa Ganduje baya ba.

“Ina so nayi kira ga jama’a da su yi watsi da duk wata sanarwa da Dawisu da yaransa suke yi akan Malam Salihu Sagjr Takai. Ba su da wata alaka da shi da zasu yi magana a madadinsa.”

“Malam Auwalu Muazu shi ne halastaccen mai magana da yawun Malam Salihu Sagir Takai kuma bai bayar da wannan sanarwa da su Dawisu suke yadawa ba.”

Daga shafin Ramadan Gwale

A safiyar yau ne mataimakin gwamnan Ganduje na fannin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai ya fitar da sanarwa cewa Malam Salihu Sagir Takai ya umarci mabiyanshi da su zabi Dr Abdullahi Umar Ganduje na jami’iyyar APC.

Masu Alaƙa  Zaben Kano: Takai yace a zabi Ganduje - Salihu Tanko Yakasai

 

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: