Na’urar tattara zabe ta INEC ta nuna Atiku ne ya lashe zaben 2019 – PDP

A bayanan da jam’iyyar PDP ta mika kara gaban kotu ranar Laraba, sun nuna cewa na’urar tattara sakamakon zabe na hukumar INEC ya nuna jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben shugaban kasa da kuri’u miliyan 1.6.

Jaridar Premimiun Times ta rawaito cewa PDP tace wannan daya ne daga cikin hujjoji 50 da jam’iyyar PDP ta mika a gaban kotun dake sauraron shari’ar zaben shugaban kasa da a Abuja.

Idan ba’a manta ba tun bayan bayyana sakamakon zaben shugaban Kasa da hukumar zabe tayi, jam’iyyar PDP ta yi watsi da wannan sakamakon inda ta kirashi da zabe mai cike da magudi.

A sakamakon da aka bayyana bayan zaben, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben da kuri’u 15,191,847 inda Atiku ya samu kuri’u 11,262,978.

Masu Alaƙa  Sakamakon zabe kai tsaye daga birnin Kano da kewaye

A bayanan korafin da PDP ta mika, ya nuna cewa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben da kuri’u 18,356,732 inda ya kada Buhari na Jam’iyyar APC da ke da kuri’u 16,741,430.

Bayan nan PDP ta ce takardan kammala jarabawar makarantan sakandare da Buhari ya mika ta boge ne domin a cewar su a lokacin babu jarabawar WASC, amma kuma ita Buhari yake gadara da.

Haka kuma lauyan Atiku da Jam’iyyar PDP ya mika wa kotu shaidar takardun watardun da aka shigar da sakamakon zabe, da wasu bayanai dake nuna yadda aka yi magudi da a wajen hada alkalumma sakamakon zaben da wasu bayanai.

Masu Alaƙa  Zaben Gwamna: Kwankwaso yaci akwatin kofar gidanshi

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: